Isa ga babban shafi

MDD zata gudanar da taro ta bidiyo saboda coronavirus

A karon farko za’a gudanar da taron Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ta kafar bidiyo saboda matsalar annobar coronavirus wadda ke cigaba da daukar rayukan jama’a.

Zauren Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York.
Zauren Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York. REUTERS/Shannon Stapleton
Talla

Shugaban Majalisar Tijjani Muhammed Bande ya aike da wasika ga jami’an Majalisar yace taron da zai gudana tsakanin 22 zuwa 29 ga watan Satumba zai kunshi nadadden jawabin shugabannin wanda za’a dinga watsa shi kai tsaye.

Bande yace ya biyo bayan hana tafiye tafiye da kuma matakan kariya daga annobar, abinda ya sa kowacce kasa zata aike da jawabin shugaban ta da aka nada na mintina 15, yayin da wakilan su dake New York zasu halaci lokacin da za’a gabatar da jawabin.

A watan jiya, Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres yace zai yi wuya shugabannin kasashen duniyar su halarci taron da aka saba gudanarwa a watan Satumba sakamakon annobar COVID-19.

A tarihin duniya dai ba’a taba soke taron Majalisar Dinkin Duniya da aka fara gudanar da shi a shekarar 1945 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.