Isa ga babban shafi
Vatican

Corona ta hana jama'a halartar hudubar Paparoma

Karon farko a tarihin cocin Katolika, yau Lahadi Paparoma Francis zai gabatar da hudubar Easter daga fadar St-Peters da ke Vatican ba tare da halartar mabiya ba, sakamakon yadda mutane ke killace a gidacensu a wannan lokaci da duniya ke yaki da annobar Covid-19.

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis zai gabatar da hudubarsa ba tare da halartar mabiya ba
Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis zai gabatar da hudubarsa ba tare da halartar mabiya ba REUTERS/Remo Casilli
Talla

Vatican ta ce taruwar jama’a don sauraren huduba da addu’o’in da Paparoma ya saba gabatarwa tare da daga wa mabiya hannu daga tagar Fadar St-Peters, duk babu wadannan abubuwa a wannan Lahadi.

A maimakon haka mabiya cocin ta Katalika da aka kiyasta cewa sun fi milyan dubu daya a sassan duniya, za su saurari Paparoma ne daga gidajensu musamman ma ta kafafen talabijin, lamarin da ke faruwa karo na farko a tarihin mujami’ar.

A ranar Asabar ma an watsa huduba da kuma addu’’o’in Paparoma ne daga Vatican kai-tsaye ta gidajen talabijin ba tare da bai wa mabiya damar halatar ba, wannan kuwa sakamakon matakan da ake dauka don hana yaduwar wannan annoba ta Coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.