Isa ga babban shafi
Coronavirus

Damisa ta kamu da cutar coronavirus a Amurka

Wata damisa da ke gidan ajiyar dabbobi na Bronx a birnin New York na Amurka ta kamu da cutar coronavirus.

Nadia,mai shekaru hudu da ta kamu da cutar coronavirus a gidan ajiyar dabbobi na Bronx dake birnin New York na Amurka
Nadia,mai shekaru hudu da ta kamu da cutar coronavirus a gidan ajiyar dabbobi na Bronx dake birnin New York na Amurka Reuters
Talla

Damisar mai suna Nadia kuma mai shekaru hudu a duniya, ta fara nuna alamomin kamuwa da cutar da suka hada da wahalar numfashi, abin da ya sa aka dauki samfurin jininta don yi mata gwaji kuma daga bisa aka tabbatar cewa, ta harbu da coronavirus.

Kodayake Kungiyar Kare Dabbobin Gandun Daji na Bronx da ke Amurka, ta ce, ana sa ran warkewar damisar , yayin da kungiyar ta ce, babu wata dabba baya ga Nadia da ta kamu da wannan cuta a gidan ajiyar dabboni.

Sai dai akwai wasu dabbobin da suka hada da zakuna da su ma suka fara nuan alamomin kamuwa da cutar, amma ba a yi musu gwaji ba kawo yanzu.

Wasu rahotanni sun ce, daya daga cikin masu kula da dabbobin ne, ya shafa wa damisar wanann cuta bayan shi ma ya kamu da ita.

A karon farko kenan da wani dan adam ke shafa wa dabbar daji cutar covid-19 a cewar Paul Calle, babban likitan dabbobi a gidan Zoo na Bronx.

Tuni dai aka kulle gidan ajiyar dabbonin na Bronx sakamakon yaduwar wannan annoba da ta yi barna matuka a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.