Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta razana shugabannin kasashen duniya

Shugabannin kasashen duniya sun razana da yadda cutar COVID 19 ko kuma Coronavirus ke yaduwa zuwa karin kasashen Turai, inda har ma aka rufe makarantu a Birtaniya.

Jamin yaki da cutar Coronavirus a China
Jamin yaki da cutar Coronavirus a China China Daily via REUTERS
Talla

A nahiyar Turai, kasar Italiya ce ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar, inda a halin da ake ciki mutane sama da 450 suka harbu da cutar, 15 kuma suka mutu, yayin da mutane 27 suka kamu da cutar a Jamus, 13 sun kamu a Faransa, sai kuma Spain da ke da mutane 13, yayin da kuma hukumomi a Denmark da Estonia suka tabbatar da bullar cutar.

A Birtaniya, inda aka tabbatar da cewa cutar ta harbi mutane 15, har ya kai ga rufe wasu makarantu, Hukumar Kula da Lafiya ta ‘yan kasar ta bayyana fargabar cewa, wadanda suka galabaita cikin masu fama da cutar na iya fuskantar matsala da zarar asibitoci sun fara samun karuwar majinyata.

A halin da ake ciki, Saudi Arabia ta dakatar da ‘yan kasashen waje da ke da kudirin ziyartar kasar don aikin Umarah, a wani mataki na kare kai daga cutar da ke ci gaba da kutsawa kasashen duniya.

A kasar Japan, Firaminista Shinzo Abe, ya bukaci makarantu a fadin kasar da su rufe na tsawon makonni, a daidai lokacin da hukumomi suka sanar da mutuwar mutum na hudu da ya harbu da cutar Coronavirus.

A China, inda cutar ta samo asali, fiye da mutane 2,700 ne suka mutu, dubu 78 suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.