An gano wani makeken rame makare da gawarwaki
A Panama, yan Sandar kasar sun gano wani makeken rame da aka binne wasu kananan yara.Binciken farko daga mahakunta ya gano cewa matsafa ne suka kashe wadanan yara a garin mai suna Terron ,a wani yankin dake da tsaunuka mai nisan kilometa 250 da babban birnin kasar.
Wallafawa ranar:
Daga cikin gawarwakin mutanen da aka tono harda wata mata mai juna biyu.
Gwamnatin kasar ta tura da jirage masu saukar ungulu dauke da sojojin da yan sanda domin kai dauki tareda taimaka wajen ceto rayukan wasu mutane 15 da matsafa ke shirin yiwa yankan rago banda haka an baiwa rundunar umurni cafke masu hannu a wannan kazamin aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu