Isa ga babban shafi
Duniya

Shugaban Iran ya musanta batun ganawa da Donald Trump

Shugaban Iran Hassan Rohani ya kawar da yiyiwar shiga tattaunawa tsakanin kasar sa da Amruka, tare da bayyana cewa kamar yadda aka tsara nan da kwanaki 2, kasar sa zata rage amfani da wani bangare na yarjejeniyar Nukiliyar da ta cimma tsakaninta da kasashen turai.

Shugaban Amurka Donald Trump da Hassan  Rouhani Shugaban kasar Iran
Shugaban Amurka Donald Trump da Hassan Rouhani Shugaban kasar Iran AFP
Talla

Téhéran da wasu kasashen turai 3 da suka hada da Faransa ,jamus, da Britaniya na ta kokarin ceto yarjejeniyar da aka cimma a 2015 da ta takaita shirin samar da makamashin nukliyar Iran, bayan ficewar Amurka daga cikinta a 2018, tare da mayar da jerin takunkuman da Amurkar ta kakabawa kasar ta Iran

Kwana guda bayan tattaunawar da ta shiga tsakanin kwarraru kasashen Faransa da Iran a birnin Paris, Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce damar da ake da ita ta son shiga tattaunawar tsakanin Iran da Amrukar a cikin gaggawa na ci gaba da kankancewa domin kuwa akwai batutuwa da dama da ya kamata a magance

Wata majiyar Diflomasiyar Faransa ta bayyana cewa, dangane da tattaunawar nukliyar za a iya cewa karara Iran ta nuna munanan alamu, idan har ta rage amfani da alkawulan da ta dauka kan aiki da yarjejeniyar Nukliyar da aka cimma a cikin wannan mako

Idan dai ba a manta ba a karshen watan jiya na Agusta ne taron gungun kasashe 7 masu karfin tattalin arzikin masana’antu na duniya G7 a Faransa, ne shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amruka suka bayyana yiyuwar yin wata ganawa tsakanin Donald Trump da shugaban Iran Hassan Rohani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.