Trump ya zargi Iran da rura rikici bayan kwace tankokin man Birtaniya
Amurka ta zargi Iran da rura wutar rikici tare da takalar fada bayan sanarwar dakarun juyin-Juya halin kasar ta Iran wadda ta yi ikirarin kwace tankokin man Birtaniya.
Wallafawa ranar:
A jawabansa gaban manema labarai, Donald Trump ya ce ba wai tank ace guda daya ko guda biyu ba, za su iya dara haka, a don haka ya zama wajibi Amurka ta taimakawa Birtaniya.
Donald Trump yayin jawabin nasa ga manema labarai, y ace zai tattaunawa da Birtaniya don sanin ta yadda zai taimaka mata.
Tun a yammacin jiya juma'a ne, jami’an da ke tafe da tankokin man na Iran suka tabbatar da cewa, an kwace iko da jirginsu kuma yanzu haka suna kan hanyar tunkarar Iran.
A bangare guda itama Birtaniya ta tabbatar da kwace mata jiragen har guda 2 a mashigin ruwan Hormuz inda ministan harkokin wajenta Jeremy Hunt, ke cewa kasar ba za su lamunci take-taken na Iran ba.
Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyar ta fitar, ta yi tir da matakin na Iran inda ta ce kwace jiragen babban abin damuwa wanda dole ne ta dauki kwararan matakai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu