Isa ga babban shafi
Afghanistan

Dakarun Amurka sun fi kisa fiye da Taliban a Afghanistan

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, a karon farko adadin fararen hular da dakarun Amurka da na kawance suka kashe a Afghanistan, ya zarce adadin da mayakan Taliban da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda suka kashe a kasar.

Wasu daga cikin dakarun Amurka a Afghanistan
Wasu daga cikin dakarun Amurka a Afghanistan Reuters/Goran Tomasevic
Talla

Rahoton na zuwa a daidai lokacin da Amurka ta kara kaimi wajen kaddamar da hare-haren jiragen sama a Afghanistan, yayinda a gefe guda take ci gaba da kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da mayakan Taliban da ke rike da sassa da dama a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a cikin watanni uku na farkon wannan shekarar ta 2019, dakarun kawancen da ke goyon bayan gwamnatin Afghanistan sun kashe fararen hula 305, yayinda kungiyoyin ‘yan ta’adda suka kashe mutane 227.

An hallaka akasarin fararen hular ne ta hanyar kaddamar da farmakin jiragen sama ko kuma ta hanyar samamen kasa da dakarun da ke samun goyon bayan Amurka suka gudanar, kuma masu aikata wannan laifin na kauce wa fuskantar hukunci kamar yadda Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce.

A shekarar 2017, dakarun sojin Amurka suka kara kaimi a aikin da suke yi a Afghanistan bayan shugaba Donald Trump ya sassuta wasu matakai da zummar bai wa dakarun na Amurka damar kaddamar da hare-hare kan sansanonin Taliban cikin sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.