Isa ga babban shafi
Amurka

iftila'in Kankara ya durkusar da jihohin Amurka

Hukumomin wasu Jihohin Amurka da ke fuskantar bala’in sanyi da dusar kankara sun gargadi miliyoyin jama’ar su da su dauki matakan kare kansu da iyalan su da kuma katse zirga zirga.Rahotanni sun ce akalla mutane miliyan 250 ke fuskantar bala’in, yayinda aka katse zirga zirga. 

Tuni dai hukumomin jihohin suka dauki matakin kulle ma'aikatu makarantu tare da hana zirga-zirgar jiragen kasa
Tuni dai hukumomin jihohin suka dauki matakin kulle ma'aikatu makarantu tare da hana zirga-zirgar jiragen kasa REUTERS/Pinar Istek
Talla

Ibtila’in sanyin da ya shafi kimanin mutane miliyan 250, ya tilasta wa hukumomi rufe makarantu da dakatar da harkokin kasuwanci baya ga tsayar da aikin isar da sakwanni ta gidan waya, yayin da aka bukaci al’umma da su ci gaba da zama a gidajensu bayan wasu jihohi sun ayyana dokar ta-baci.

Rahotanni na cewa, tsananin sanyin a Chicago da ya kasance birni na uku mafi girma a Amurka, ya zarce sanyin wani bangare na yankin Antarctica bayan ma’auninsa ya yi kasa da maki 22 na Celsius.

Sama da zirga-zirgar jirage 1 da 500 aka soke a manyan filayen jiragen sama da ke birnin, baya ga dakatar da ayyukan jiragen kasa.

A can Indiana da Michigan da Illinois da Ohio duk, an dakatar da aika sakwanningidan waya sakamakon ibtila’in sanyin da masana hasashen yanayi suka bayyana a matsayin wanda ke aukuwa sau daya a tarihin al’umma.

Mahukuntan Amurka sun gargadi cewa, sanyin na barazana matuka ga rayuwa, kuma a wasu jihohin an tanadar wa tsofaffi da masu nakasa dakunan dumi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.