Bukukuwan Kirismeti a sassan duniya
Kiristoci a sassan duniya na gudanar da bukukuwan kirismeti domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu, inda aka gudanar da addu’o’i a muhimman wurare da suka hada da Bethleem, Jerusalem, Vatican da ma sauran mujami’o’i a daren da ya gabata.
Wallafawa ranar:
A garin Bethlehem da ke cikin Palesdinu inda aka haifi Yesu Almasihu, dubban mutane ne suka taru domin raya daren jiya ta hanyar addu’o’I da kuma nuna farin ciki.
Wani lokaci a yau kuwa shugaban mabiya darikar Katolika a duniya Paparoma Francis zai jagoranci addu’o’I na shekara-shekara tare da gabatar da jawabi zuwa ga mabiya a sassan duniya, domin bayyana muhimmancin wannan rana da kuma sakon da kunshe a cikinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu