Duniya na gudanar da bukukuwan Kirismeti
Jagoran mabiya darikar Katotlika na duniya Paparoma Francis, wanda ke gabatar da jawabin ranar Krismeti daga dandalin St Peters, ya yi kakkausar suka a game da yawaitar tashe tashen hankula a sassa daban daban na duniya, tare da yin kira da a kawo karshen muzgunawar da ake yi wa tsirarun kiristoci musamman a Iraki da kuma Syria.
Wallafawa ranar:
Francis wanda ke jagorantar addu’o’in kirismeti karo na biyu a tarihi, ya kuma bukaci a shiga tattaunawar da za ta iya samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palastinu, kamar dai yadda ya bukaci a kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar Ukraine.
Har ila yau jagoran na cocin katalika ya nuna damuwa a game da halin da ake ciki a wasu kasashen Afirka, musamman Najeriya da jamhuriyar Afirka ta tsakiya, sannan ya jajantawa al’ummomin kasashen Liberia, Sierra Leone da kuma Guinee Conakry da ke fama da cutar Ebola.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu