Isa ga babban shafi
MDD

Cin zarafin mata abin kunya ne a tsakanin al'umma- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cin zarafin mata a matsayin abin kunyar da ya mamaye al’umma, in da take cewa muddin mata da 'yam mata ba su samu 'yancin rayuwa cikin walwala ba, duniya ba za yi tinkaho da samar da daidaton jinsi ba. 

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata a duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata a duniya Asia Times
Talla

Sakatare Janar na Majalisar, Antonio Guterres ya bayyana haka wajen wani taro na musamman na yaki da cin zarafin mata, in da yake cewa yanzu haka matsalar ta zama ruwan dare gama duniya.

Guterres ya ce, abin kunya ne ga daukacin al’umma yadda suke kawar da kai lokacin da ake cin zarafin 'yan mata da mata, matakin da ke karo da shirin Majalisar DInkin Duniya na cimma muradun karni.

Sakataren ya bayyana cin zarafin mata a matsayin take hakkin bil'adama, kuma ana samun matsalar ta nau’oi daban daban da suka hada da dukan mata a gida da yi musu fyade da azabtar da su da yi musu kaciya da makamantan haka.

Jami’in ya kara da cewa, irin wannan cin zarafin kan yi matukar illa ga rayuwar matan  ta hanyar hana su walwala a cikin jama’a da kuma sakewa wajen kokarin cimma bukatunsu.

Guterres ya bukaci hukumomi da kungiyoyi da su sake dagewa wajen ganin an shawo kan wadannan matsaloli da ke matukar illa ga jama’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.