Isa ga babban shafi
Isra'ila-Palestine

Rikici ya tsananta tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Sabon tashin hankalin da aka samu tsakanin Israila da Falasdinawa na yi wa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla barazana, ganin yadda aka kwashe daren jiya ana dauki ba dadi tsaknain bangaroirin biyu.

Tashin gobara bayan wani harin sama da sojin Isra'ila suka kai wa Falasdinawa
Tashin gobara bayan wani harin sama da sojin Isra'ila suka kai wa Falasdinawa REUTERS/Ahmed Zakot TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Israila ta ce, ta kakkabo makaman roka akalla 100 daga cikin sama da 370 da kungiyar Hamas ta harba ma ta, yayin da ita kuma ta kai hare-haren sama da jiragen yaki, in da ta kashe Falasdinawa uku da kuma lalata tashar talabijin ta Hamas.

Jami’an lafiya sun ce, akalla Yahudawa 20 suka samu rauni daga rokar da Hamas ta harba.

Sabon rikicin na zuwa ne bayan wanda aka kwashe watannin ana yi akan iyakar Gaza da Isra'ila, lamarin da ya sanadiyar mutuwar Falasdinawa da dama.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya katse ziyarar da yake gudanarwa a birnin Paris na Faransa domin komawa gida sakamakon sabon rikicin wanda ya fara tun a ranar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.