Isa ga babban shafi
Trump - Putin

Trump ya bukaci ganawa da Putin na Rasha

Shugaban Amurka Donald Trump na fatan ganawa da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin a haduwar da za su yi a birnin Paris ranar 11 ga watan Nuwamba yayin bikin tunawa da Yakin Duniya Na 1.A jawaban da John Bolton mashawarcin shugaban na Amurka kan harkokin tsaro ya gabatar ya ce Donald Trump ya sanar da shi bukatar da ya ke da ita a ganawa da Vladimir Putin. 

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump yayin ganawarsu ta watan Yuli a Helsinki.
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump yayin ganawarsu ta watan Yuli a Helsinki. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Shugabannin biyu za su kasance ne birnin Paris tare wasu shugabannin kasashen duniya 60, ranar 11 ga watan Nuwamba don bikin cika shekaru 100 da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Duniya na biyu.

A watan Yuli ne Trump da Putin suka yi ganawar farko a Helsinki, wadda bayan ganawar ce Trump ya fuskanci kakkausar suka a gida sakamakon sassaucin da yayi a huldar ta sa da takwaransa na Rasha.

John Bolton ya shaida shugaba Putin cewa, shugaba Trump zai so ya gana da shi a wajen taron, yayinda shugaban Rashan ya ce, yana da mahimmanci, kuma zai yiwu a samu wata magama ta ganawa, inda ya kara da cewa ganawarsa da shugaban Amurkan zai kasance da matukar amfani.

A ranar Litinin wannan makon, sai da Bolton ya gana da jami’an Rasha a Moscow kafin wannan ganawarsa da shugaban na Rasha.

Ziyarar tasa ta biyo bayan sanarwar da Trump ya yi na janyewar Amurka daga yarjejeniyar makaman nukiliya masu cin matsakaicin zango, wadda aka cimma tun zamanin yakin cacar baka tsakanin tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan, da Mikhail Gorbachev, shugaban rusasshiyar Tarayyar Soviet na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.