Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

An bude taron kasuwancin kasa da kasa a Saudiya

Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad Bin Salman ya gabatar da jawabansa na bude babban taron kasuwanci da zuba jari na kwanaki 3 da Kasar ke karbar bakoncin dubban hamshakan ‘yan kasuwa daga sassan duniya ba tare da nuna wata alamar damuwa tattare da shi ba, duk kuwa da batun kisan fitaccen dan jaridar kasar Jamal Kashoggi a Turkiyya da ya haddasa kauracewar wasu ‘yan kasuwa a taron.

An dai gano Muhammad Bin Salman cike da murmushi yana daukar hoto da mahalarta taron duk kuwa da dambarwar kisan Jamal Kashoggi da ake yi kansa.
An dai gano Muhammad Bin Salman cike da murmushi yana daukar hoto da mahalarta taron duk kuwa da dambarwar kisan Jamal Kashoggi da ake yi kansa. SAUDI-BINLADIN/FALL Bandar Algaloud/Courtesy of Saudi Royal Cour
Talla

Muhammad bin Salman wanda ya gabatar da jawabin mintuna 15 na bude taron an gano shi yana daukar hoto da mahalarta taron cike da fara’a da ke nuna ba abin da ke damunsa duk kuwa da batun kisan Jamal Kashoggi da ake ganin akwai hannunsa a kisan la’akari da yadda dan jaridar ya yi kaurin suna wajen sukar gidan sarautar kasar.

Taron wanda ke da nufin fadada harkokin kasuwancin kasar ta Saudi Arabia da ta shafe shekaru ta na dogaro da bangaren man fetur kafin zuwan Yarima Muhammad bin Salman da ya sha alwashin baza komar tattalin arzikin kasar tare da sauke ta daga turbar dogaro da dangogin mai kadan.

Ko da dai taron ya gamu da cikas na rashin halartar wasu daga cikin abokanan huldar Saudiyyan sakamakon batun kisan Kashoggi da ake zargin kasar da aikatawa a Ofishin jakadancinta na birnin Santambul, Yariman ya sanar da yarjejeniyar kasuwanci ta akalla dala biliyan 50.

Sai dai ministan ma’adinai na kasar Khalid al-Falih ya ce Saudiya na cikin wani hali da kawayenta na gaskiya ne kadai suka iya mara mata baya sakamakon zargin kisan na Kashoggi wanda ya yi yakinin cewa babu hannun Yariman na su a ciki.

Ka zalika Al-Falih ya yaba da kokarin kawayensu da suka ture duk wata jita-jita tare da halartar taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.