Isa ga babban shafi
Amurka

Kavanaugh ya sake shiga tsaka mai wuya a Amurka

Kwanaki 4 kafin wata mata mai suna Christine Blasey Ford ta bayar da shaida a gaban kwamitin Majalisar Dattawan Amurka dangane da zargin aikata lalata, wata matar mai suna Deborah Ramirez mai shekaru 53 a duniya ta ce, ita ma ta fuskanci irin wannan barazar daga Brett Kavanaugh, wanda Donald Trump ke son nadawa a matsayin alkalin kotun kolin kasar.

Brett Kavanaugh na cikin tsaka mai wuya a dai dai lokacin da yake dakon Majalisar Dattawan Amurka ta tabbatar da shi kan mukamin alkalin kotun koli
Brett Kavanaugh na cikin tsaka mai wuya a dai dai lokacin da yake dakon Majalisar Dattawan Amurka ta tabbatar da shi kan mukamin alkalin kotun koli REUTERS/Chris Wattie -/File Photo
Talla

Deborah Ramirez ta shaida wa New York Times cewa lamarin ya faru ne yayin wani biki a wata makarantar sakadanre a lokacin tana da shekaru 15 yayin da shi kuma Kavanaugh ke da shekaru 17 a duniya.

Sai dai Kavanaugh ya musanta dukkanin zarge-zargen tare da bayyana yunkurin bata masa suna.

Ana bukatar amincewar mambobi 21 na kwamitin Majalisar Dattawa da kuma daukacin ‘yan Majalisar kafin nada Kavanaugh a matsayin alkalin kotun kolin kasar.

Wasu ‘ya’yan jam’iyyar Republican da shugaba Donald Trump sun zargi Ford da wasu ‘ya’yan jam’iyyar Democrat da kokarin haifar da tarnaki wajen tabbatar da Kavanaugh akan wannan mukami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.