Isa ga babban shafi
Myanmar

Myanmar ta daure 'yan jaridar Reuters shekaru 7

Wata kotu a Myanmar ta daure ‘yan jarida 2 na Kamfanin Dillancin Labaran Reuters shekaru bakwai a gidan yari bayan ta same su da laifin keta doka a yayin gudanar da aikinsu na bincike kan rikicin kabilar Rohingya.

Ana kallon shari'ar 'yan jaridar a matsayin gwajin-dafi ga ingancin 'yancin fadin albarkacin baki a Myanmar
Ana kallon shari'ar 'yan jaridar a matsayin gwajin-dafi ga ingancin 'yancin fadin albarkacin baki a Myanmar REUTERS/Ann Wang
Talla

An kama Wa Lone da Kyaw Soe Oo, dukkaninsu ‘yan asalin Myanmar duk da cewa suna dauke da takardun izini da jami’an ‘yan sanda suka ba su don gudanar da aikinsu.

‘Yan jaridar sun musanta taka doka tare da zargin jami’an ‘yan sanda da dana musu tarko.

Mutanen biyu sun shafe tsawon lokaci suna tattara hujjoji kan kisan da sojojin kasar suka yi wa wasu mutane 10 a kauyen Inn Din da ke jihar Rakhine.

Sun samu takardun izini daga jami’an ‘yan sanda, amma aka cafke su nan take kan mallakar wadannan takardu.

Ana kallon shari’ar ‘yan jaridar a matsayin gwajin dafi ga ingancin ‘yancin fadin albarkacin baki a Myanmar.

Tun a shekarar 2017 ne ake tsare da ‘yan jaridar a gidan yari kuma dukkaninsu na da iyalai da kanana yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.