Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela ta kama 'yan ta'addan da suka kai wa Maduro hari

Gwamnatin Venezuela ta sanar da kama 'yan ta’adda guda 6 da ake zargi da kokarin hallaka shugaban kasa, Nicolas Maduro lokacin da yake jawabi a gaban daruruwan sojojin kasar.

Shugaba Nicolas Maduro da aka yi yunkurin hallakawa a Venezuela
Shugaba Nicolas Maduro da aka yi yunkurin hallakawa a Venezuela REUTERS
Talla

Ministan Cikin Gida da Shari’a, Nestor Reverol ya sanar da kama mutanen a wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin, yayin da ya sanar cewa, sojoji 3 da suka samu rauni na cikin mawuyacin hali, amma tuni aka sallami wasu daga asibiti.

Shugaba Maduro ya zargi Amurka da Colombia da kitsa kai masa harin wanda aka yi amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu wajen kaddamarwa, zargin da kasashen biyu suka yi watsi da shi, yayin da daga bisani wasu gungun ‘yan tawayen kasar ta Venezuela suka dauki alhakin harin.

A cewar mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro, John Bolton, akwai yiwuwar gwamnatin shugaba Maduron ce ta shirya kai harin na karya domin cimma wani buri da ita ce kadai za ta iya fayyace shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.