Chile na tuhumar limaman Katolik 158 da boye laifukan cin zarafi
Hukumomin Kasar Chile sun ce suna gudanar da bincike kan shugabannin mabiya darikar Katolika 158 da suka hada da Bishop Bishop da masu bushara saboda zargin da ake musu na boye bayanai kan yadda aka dinga cin zarafin yara maza da manya a cocin.
Wallafawa ranar:
Mai Gabatar da kara, Luis Torres, ya ce binciken ya biyo bayan korafe korafe 144 da aka gudanar da bincike akai da ya shafi mutane 266, cikin su harda yara 178.
Torres ya ce binciken ya faro ne tun daga shekarar 1960, inda aka gano batutuwa da dama masu alaka da cin zarafin Mata, kananan yara dama manyan mabiyan darikar ta Katolika.
Ko a baya-bayan nan sai da shugaban darikar na duniya Fafaroma Francis ya karbi takardun murabus na wasu manyan shugabannin cocin kasar kan makamantan zarg-zargen.
Francis ya bayyana zarge-zargen kan limaman da wani batu da ke kokarin zubar da kimar shugabancinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu