Isa ga babban shafi

Faransa ta gargadi Amurka kan haddasa rudani a fagen kasuwanci

Ministan Kudin kasar Faransa Bruno le Maire, ya ce kasashen turai ba zasu fara tunanin tattaunawa da Amurka kan yarjejeniyar cinikayyar bai daya ba, har sai ta janye harajin da ta sanyawa kayan karafa da Aluminium da kasashen turan ke kaiwa kasuwanninta.

Ministan Kudin kasar Faransa  Bruno Le Maire.
Ministan Kudin kasar Faransa Bruno Le Maire. Eric Peirmont/ AFP/Getty Images
Talla

Ministan kudin na Faransa ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Argentina, inda ake taron ministocin kudi na kungiyar G20, kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Bruno Le Maire, ya kuma gargadi Amurka da ta guji tafka kuskuren haddasa rudani a fagen huldar cinikayya tsakanin kasashen duniya, wanda zai haddasawa tattalin arzikin kasashen nakasu.

Gargadin dai ya zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar sake kakaba sabon haraji kan kayayyakin da China ke kai wa kasarsa da darajarsu za ta kai dala biliyan 500.

A watan Yunin da ya gabata shugaba Trump ya sanar da kakaba harajin kashi 25 akan kayayyakin da kasar China ke shigarwa Amurka, da darajarsu ta kai ta dala biliyan 50, inda ya ce matakin ya zama tilas a dalilin yadda kasar ta China ke satar fasahohin kayayyaki daban daban da Amurka ke kerawa.

Sai dai duk da cewa Trump ya gargadi China da kada ta kuskura da mayar da martani, sa’o’i bayan kakabawa kayan nata haraji, itama China, ta zayyana kayayyakin da Amurka ke kai wa cikinta akalla 659, cikin har da kayan amfanin gona, da kuma motoci, masu darajar dala bliyan 50, wadanda ta kakabawa harajin kashi 25.

Trump dade yana zargin China da wasu kasashen Turai da yi wa kamfanonin Amurka, ma’aikata da kuma manomanta barazana ta hanyar aikata ha’ainci a alakar kasuwancin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.