Isa ga babban shafi
India

Maza 17 sun yi wa 'yar shekara 11 fyade

Rundunar ‘yan sandan India ta cafke maza 17 da ake zargi da yi wa wata karamar yarinya mai shekaru 11 fyade na tsawon makwanni, abin da ya tayar da hankulan al’ummar kasar.

Kungiyoyin Kare Hakkin Mata na kokarin yaki da matsalar yi wa mata da 'yan mata fyade a India
Kungiyoyin Kare Hakkin Mata na kokarin yaki da matsalar yi wa mata da 'yan mata fyade a India SAJJAD HUSSAIN / AFP
Talla

Rahotanni na cewa, yarinyar na da matsalar ji, kuma an yi ma ta fyaden ne a wani sashen babban gida da ba a tare ba a kudancin birnin Chennai.

Daga cikin wadanda aka kama har da mai gadin gidan wanda ke da sassa 300 da mai gyaran famfo da kuma jami’in da ke kula da akwatin daga mutane daga kasa zuwa sama wato “Lift.”

Jami’in kula da akwatin mai shekaru 66, shi ne ya fara far wa yarinyar bayan ta dawo daga makaranta, yayin da take zirga-zirga akan kekenta a harabar gidan kamar yadda ‘yan sanda suka ce.

Kazalika, jami’in ne ya gayyato sauran kattan da suka yi ta yi wa yarinyar fyade daya bayan daya tare da daukan hotonta a yayin aikata ta'asar.

Har ila yau, mutanen sun yi wa yarinyar allura, sannan suka daddaka ma ta kwayoyin bacci.

Kasar India ta yi kaurin suna wajen yi wa mata da kananan yara fyade, in da a shekarar 2016 rahotanni suka nuna cewa, kananan yara dubu 19 aka yi fyade a sassan kasar, yayin da aka kaddamar da dokar kisa kan duk wanda ya yi wa ‘yar kasa da shekara 12 fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.