Isa ga babban shafi
Amurka-Turai

Donald Trump ya caccaki Theresa May

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Firaministan Birtaniya Theresa May kan shirin ta na ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turai a ziyarar aikin da ya kai kasar, inda yake cewa shirin na iya yin illa ga dangantakar kasuwanci tsakanin Birtaniya da Amurka.

Donald Trump Shugaban Amurka
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Yves Herman
Talla

A hirar da ya yi da jaridar The Sun, Trump ya bayyana tsohon Sakataren harkokin wajen Birtaniya da ya sauka daga mukamin sa a makon jiya, Boris Johnson a matsayin wanda zai dace da mukamin Firaminista, yayin da ya soki Magajin garin birnin London kan zanga zangar da aka fara domin rashin amincewa da ziyarar da yake yi.

Yan lokuta da isowar Trump Birtaniya, mazauna Birtaniya suka fara shirya zanga zangar adawa da ziyarar ta shugaba Trump wanda kalaman sa kan batutuwa da dama suka yi hannun riga kan manufofin kasar da kuma zamantakewar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.