Trump zai kawo karshen atisayin Sojan Amurka a Koriya
Shirin Shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen atisayen sojin hadin gwiwa da Amurka da Koriya ta Kudu keyi ya baiwa manyan jami’an ma’aikatar tsaron kasar mamaki.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Donald Trump ya bayyana matakin ne a wani yunkuri na jaddada aniyar sa ta baiwa Koriya ta Arewa karfin gwiwa kan shirin bude wani sabon babi tsakanin dangantakar kasashen biyu.
Rahotanni daga Koriya ta Arewa sun ce shugaba Kim Jong Un ya amince da gayyatar da Trump ya yi masa zuwa Washington nan gaba.
Haka zalika Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya gayyaci Shugaba Donald Trump zuwa kasar Koriya ta Arewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu