Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta tsawaita takunkuman Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar amincewa da tsawaita takunkumai kan Sudan ta kudu har zuwa tsakiyar watan Yuli tare da haramta tafiye-tafiye kan shugabanninta 6 baya ga kulle asusun ajiyarsu, matukar basu yi kokarin kawo karshen rikicin kasar nan da ranar 30 ga watan Yuni ba.

Sudan ta kudu ta tsunduma yakin basasa sanadiyyar rikicin siyasa wanda ya juye zuwa kabilanci shekara guda bayan samun ‘yancin a shekarar 2011.
Sudan ta kudu ta tsunduma yakin basasa sanadiyyar rikicin siyasa wanda ya juye zuwa kabilanci shekara guda bayan samun ‘yancin a shekarar 2011. REUTERS/Jok Solomon
Talla

Gabanin zaman dai jakadan Ethiopia a majalisar ya ce ya fahimci dalilin da ya Amurka ke kokarin tsawaita takunkumin kuma kasarsa ba ta goyon baya.

Jagororin Sudan ta kudun 6 da Majalisar za ta haramtawa tafiye-tafiye tare da kulle asusun ajiyarsu sun hadar da ministan tsaro Kuol Manyang, da tsohon babban hafson sojin kasar Paul Malong.

Sauran sun hada da ministan yada labarai Michael Lueth da shugaban sashen sarrafa makamai Malek Reuben da kuma Riak Rengu sai Gwamnan Bieh Koang Rambang.

Sudan ta kudu ta tsunduma yakin basasa sanadiyyar rikicin siyasa wanda ya juye zuwa kabilanci shekara guda bayan samun ‘yancin a shekarar 2011.

Yanzu haka dai rikicin wanda ya samo asali tsakanin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar ya haddasa asarar dubban rayuka baya ga sabbaba yunwa da kuma tilastawa miliyoyin ‘yan kasar gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.