Isa ga babban shafi
AMurka- korea

Trump da Moon sun gana kan barazanar Korea ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Kudu, Moon Jae-in sun tattauna kan barazanar da Korea ta Arewa ta yi ta soke ganawa tsakanin shugaba Kim Jong-un da Trump. A gobe Talata ne Mr. Trump zai karbi bakwancin Moon a birnin Washington don zantawa kan makomar ganawa da Kim a watan gobe.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kimn Jon-un
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kimn Jon-un 路透社
Talla

Bayan kwashe tsawon makwanni na musayar zafafan kalamai da cin dunduniyar juna, kwasam Kasar Korea ta Arewa ta yi barazanar janyewa daga ganawar da aka shirya gudanarwa tsakanin Kim Jon-un da Donald Trump a cikin watan gobe saboda yadda Amurkan ke ci gaba da matsin lambar ganin Korea ta Arewa ta yi wasti da makamanta na nukiliya.

Kazalika Korea ta Arewa ta soke wata muhimmiyar ganawa tsakanita da makawabciyarta Korea ta Kudu don nuna adawa da wani atsiayen sojin hadin gwiwa da ya gudana tsakanin Korea ta Arewa da Amurka

A wata tattaunawa ta wayar tarho, shugaba Trump da Moon sun yi musayar ra’ayoyi kan matakan da Korea ta Arewa ta dauka a ‘yan kwanakin nan kamar yadda ofishin Moon ya sanar a jiya Lahadi.

Shugabannin biyu sun amince su yi aiki tare don ganin an samu nasarar gudanar da gagarumar ganawar tsakanin Trump da Kim a ranar 12 ga watan Juni a Singapore, tattaunawar da ake ganin za ta kasance ta farko tsakanin wani shugaban Amurka mai ci da kuma wani shugaban Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.