Shugaban Kamaru Paul Biya na ziyarar aiki kasar China
Shugaban Kamaru Paul Biya na ziyarar aiki a kasar China da zummar janyo hankulan masu zuba jari zuwa kasar sa.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban Kamaru ta ce ziyarar za ta taimaka wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ma’aikatar tattalin arzikin Kamaru ta ce tun ranar lahadi shugaba Biya ya isa Beijing amma kuma a yau alhamis ne zai fara gana da mahukuntan China da kuma ‘Yan kasuwa.
Kawo yanzu dai China ce babbar abokiyar cinikin Kamaru, inda alkalumma ke nuni da cewa a shekarar 2015 an samu cinikin da ya kai sama da Dala biliyan biyu da rabi tsakanin kasashen biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu