Isa ga babban shafi
Falasdinu

An kai wa Firaministan Falasdinu hari a Gaza

An kaddamar da farmaki kan ayarin motocin firaministan Falasdinu, Rami Hamdalla a yayin ziyarsa a yankin Gaza a wannan Talata, abin da ya yi sanadiyar raunata mutane akalla bakwai.

Firaministan Falasdinu Rami Hamdallah
Firaministan Falasdinu Rami Hamdallah REUTERS/Mohamad Torokman
Talla

Hamdalla da ya kai ziyarar ta musamman a yankin da ke karkashin ikon kungiyar Hamas, ya tsira da lafiyarsa a harin kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar.

Babban jami’in musayar bayanan sirri na Falasdinu, Majid Faraj na cikin tawagar da aka kai wa harin, amma shi ma ya tsira da lafiyarsa.

Wata sanarwa da aka watsa ta kafafen yada labaran gwamnatin Falasdinu ta ce, shugaba Mahmud Abbas ya bayyana harin a matsayin na matsorata, in da kuma ya zargi abokan hamayyarsa na Hamas da kitsawa.

Kawo yanzu dai babu wani bangare da ya dauki alhakin kaddamar da farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.