Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai gana da Kamfanonin 140 gabanin taron tattalin arziki

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na shirin karban jiga-jigan manyan shugabannin kamfanoni da ga sassan duniya akalla 140, gabanin babban taron ‘yan kasuwa na duniya da ke tafe a Davos na Switzerland.

Ana saran shugaban zai gabatar da sabbin manufofinsa kan tattalin arziki da za su ci karo dana takwaransa na Amurka Donald Trump.
Ana saran shugaban zai gabatar da sabbin manufofinsa kan tattalin arziki da za su ci karo dana takwaransa na Amurka Donald Trump. REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

A makon gobe ne za’a gudanar da wannan taro da aka saba yi a duk shekara da aka radawa suna World Economic Forum, inda manyan ‘yan kasuwa da shugabannin kasashen duniya za su halarta domin tattauna harkokin kasuwanci da tattalin arziki na duniya.

Ganin wannan taro da ke tafe ne shugaban Faransa zai yi amfani da wannan dama domin tattaunawa da su da burin ganin sun tsaida matsaya guda gabanin babban taron na duniya.

Haka zalika yayin taron, ana saran shugaba Macron zai gabatar da manufofinsa kan tattalin arzikin Duniya da za su ci karo dana shugaban Amurka Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.