Isa ga babban shafi
France

Merkel da Macron za su kalubalanci Trump kan Tattalin Arziki

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta mara baya ga takwaranta na Faransa, Emmanuel Macron kan manufofinsu yayin jawabi a taron tattalin arziki na  birnin Davos da ke Switzerland cikin wannan watan.Yayin taron ana kyautata zaton manufofin manyan kasashen duniya kan tattalin arziki zai sha bamban da wanda shugaban Amurka Donald Trump zai gabatar. 

Shuagabannin biyu ta Jamus Angele Merkel da takwaranta na Faransa Emmanuel Macron za su hade kai wajen sanar da manufofin tattalin arziki daya wanda ake kyautata zaton zai sha bamban dana shugaban Amurka Donald Trump.
Shuagabannin biyu ta Jamus Angele Merkel da takwaranta na Faransa Emmanuel Macron za su hade kai wajen sanar da manufofin tattalin arziki daya wanda ake kyautata zaton zai sha bamban dana shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Yves Herman
Talla

Kafin yanzu, an yi hasashen rashin halartar Angela Merkel taron na Davos wanda zai samu halartar shugabannin kasashen duniya da manyan jami’an bankuna da ‘yan kasuwa don tattaunawa kan tattalin arziki.

Sai dai bayan da ta cimma wata matsaya a ranar Juma'ar da ta gabata wadda za ta kai ga kafa gwamnatin hadaka, Jamus ta fito a hukumance ta bayyana cewa Merkel za ta halarci taron na Davos.

Akwai yiwuwar cewa Merkel za ta gabatar da jawabanta ne rana guda da  takwaranta na Faransa Emmanuel Macron bayan bude taron kafin daga bisani kuma shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da na shi kwana biyu bayan nasu a ranar da za a karkare taron.

Taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 23 zuwa 26 ga watan da muke ciki na Janairu zai samu halartar akalla shugabannin kasashen duniya 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.