Isa ga babban shafi
amurka

Trump ya caccaki May bayan zarginsa da kyamar Musulunci

Shugaban Amurka Donald Trump ya fito karara ya soki Firaministar Birtaniya Theresa May bayan wani korafi da ta yi kan kan yadda shugaban ya aike da wasu sakonnin bidiyo da ke nuna kyamar Musulmi. Trump wanda ya soki Firaministar a wani sakon twitter da ya wallafa ya caccaki kalaman da mai magana da yawunta ya yi da ya nuna rashin dacewar bidiyon nuna kiyayya ga musulmi da shugaban ke yadawa.

Tuni dai aikewa da sako bidiyon ya janyowa shugaba Trump munanan suka a ciki da wajen Amurka, saboda zargin da ake masa na kokarin raba kan jama’a da kuma haddasa rikici.
Tuni dai aikewa da sako bidiyon ya janyowa shugaba Trump munanan suka a ciki da wajen Amurka, saboda zargin da ake masa na kokarin raba kan jama’a da kuma haddasa rikici. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A Sakon twitter baya-bayanan da ya aike shugaba Trump, ya Ambato Theresa may inda yake cewa kar ta kar-kata a kansa ta mayar da hankali kan tsatsauran kishin addini Islama da ke barzanar ta’addanci a Ingila.

Batun da ya haifar da cacar-baka a Burtaiya da ta fuskanci hare-hare ta’addanci.

Kallaman Trump martani ne ga sukar da May ta yi na sake wallafa sakon Twitter da ke nuna kyama ga addini Islama da wata Jayda Fransen, mataimakiyar shugabar kungiyar Britain First ta yi. Wanda May ke gani bai dace ace shugaban kasa ya aikata hakan ba.

Hotunan bidiyon sun nuna yadda Musulmai ke ruguza wani mutum-mutumi kirista da kashe wani yaro da kuma far wa wani nakassashe.

Tuni dai aikewa da bidiyon ya janyowa shugaba Trump mumunar suka daga ciki da wajen Amurka, saboda zargin da ake masa na kokarin raba kan jama’a da kuma haddasa rikici.

A baya dai kotu ta taba hukunta Fransen kan samunta da laifin furta kalaman cin zarafi da batanci ga Musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.