Isa ga babban shafi
Duniya

An kera mota mai hasashen yanayin da Direba ke ciki

Kamfanin kera motoci na Toyota ya ce nan da ‘yan kwanaki zai bayyana motar da ya kera, irin ta ta farko da za ta rika hasashen yanayin da Direba ke ciki misali na barci ko damuwa, tare da kuma taimakawa direban kaucewa daga hadari.

Kamfanin na Toyota ya ce ya kera motar ce domin amfani da ita a cikin biranen da suka fiye cikowa.
Kamfanin na Toyota ya ce ya kera motar ce domin amfani da ita a cikin biranen da suka fiye cikowa. REUTERS/Francois Lenoir/Files
Talla

Kamfanin na Toyota ya ce ya kera motar ce domin amfani da ita a cikin biranen da suka fiye cikowa, wadda za ta rika taimakawa tsofaffi ko wadanda suke fama da nakasa wajen zirga zirga.

Mujallar da ake wallafawa kan kere-keren da suka shafi na motoci a turai ta “Automative News” ta ce a makonnan da muke ciki ne za’a nuna motar a birnin Tokyo na Japan.

Wasu daga cikin ayyukan da motar ta kebanta da su shi ne ganowa, ko kuma hasashen cewa Direba ya gaji, ko yana jin barci ko fushi, ta hanyar lura da motsin idanun direba, yanayin fuskarsa, da kuma motsin jikinsa. To sai dai bayan nuna wannan mota, sai a shekara ta 2020 za’a fara amfani da wannan mota.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.