Isa ga babban shafi
Iran

Yarjejeniyar nukiliyar Iran na bukatar ginshikai uku- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya goyi bayan ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya 6, amma ya bukaci a samarma ta wasu karin ginshikai guda uku.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. 路透社
Talla

A lokacin da ya ke magana a gaban manema labarai a daura da taron Majalisar Dinkin Duniya, shugana Macron ya ce, ana iya ci gaba da aiki da yarjejeniyar ta 2015, domin kuwa yarjejeniya ce mai kyau da ta bada damar zura ido sosai a yanayin da ake ciki a yanzu.

“Ya kuma kamata mu kara wasu ginshikai biyu zuwa uku domin kara karfafa tsayuwar yarjejeniyar ba wai rusa ta ba” in ji Macron.

Ginshikan da shugaban na Faransa ya bayyana sun hada da kara sanya ido kan makaman Iran masu cin dogon zango da kuma ayukan kere-kerenta da ba su shigo cikin yarjejeniyar ba.

Ginshigi na biyu shi ne tsawaita rayuwar yarjejeniyar har bayan shekara ta 2025 domin a cewar Macron, aikin yarjejeniyar za ta kare ne bayan 2025.

Sai kuma ginshiki na uku da Macron ya ajiye a matsayin buda tattaunawa kai tsaye da Iran kan yadda za a kawo karshen halin da yankin gabas ta tsakkiya ya tsinci kansa ciki a yau.

“Amma baya ga haka, babban kuskure ne watsar da yarjejeniyar ba tare da an samar da wadda ta fita ba” in ji Macron.

Shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da nuna adawa da yarjejeniyar wadda aka cimma a lokacin Barack Obama da ya gada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.