Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Diflomasiyya : Faransa ta sha gaban Amurka a karfin fada aji

Faransa ta sha gaban Amurka da Birtaniya a Karfin fada aji ta fuskar diflomasiya ba tare da nuna karfin soji ba, kamar yadda wani sakamakon bincike ya nuna. binciken ya ce shugaba Emanuel Macron ne ya daga darajar Faransa kan sauran manyan kasashen.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Ian Langsdon
Talla

A binciken da wani kamfanin hulda da jama’a da kuma jami’ar kudancin califonia a Amurka suka gudanar ya nuna cewa Faransa ce kan gaba a karfin fada aji ba tare da amfani da karfin soji ba.

Amurka da ke matsayi na daya a bara, a bana ta koma matsayi na uku, kuma binciken ya nuna cewa salon mulkin trump ya yi tasiri ga koma-bayan kasar.

Binciken ya yi amfani da karfin kasashe wajen hada kawance tare da yin tasiri ga sauran kasashe.

An tattara bayanai ne na kasashe 25 domin auna girman karfin su a duniya ta hanyar lalama.

Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su sun hada da janyo ra’ayin dalibai na wasu kasasshe zuwa karatu a jamio’in manyan kasashen da janyo hankalin ‘yan yawo bude.

Faransa da ke matsayi na 5 a bara, a lokacin da Francios Holande ke mulki, binciken ya ce ci gaban kasar a y nau ya faru ne sakamakon zaben Macron sabo a siyasar Faransa.

Binciken y ace duk hare haren ta’addancin da Faransa ke fuskanta amma hakan bai hanawa baki da dalibai ci gaba da tururuwa ba kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.