Isa ga babban shafi
Ramadan

Asabar za a soma Azumi a Saudiya

Hukumomin Kasashen Saudiya da Daular Larabawa sun bayyana cewar a ranar Asabar za su fara azumin watan Ramadan bayan kasa ganin jinjirin watan a yau Alhamis.

Asabar za a soma Azumi a Saudiya  da Daular larabawa
Asabar za a soma Azumi a Saudiya da Daular larabawa iStock photo
Talla

Sanarwar da hukumomin kasashen biyu suka bayar ta nuna cewar ba a ga jinjirin watan Ramadan yau Alhamis ba, saboda haka watan Sha'aban zai cika 30 gobe Juma’a, kuma ranar Asabar za ta kasance daya ga watan Ramadan.

Kasar Lebanon ta bayyana ranar asabar a matsayin ranar da za a tashi da Azumin Ramadan a kasar.

Zuwa yanzu babu sanarwa da ta fito daga kasar Iran.

A Najeriya tun a jiya Laraba mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayar da umurnin fara dibon watan na Ramadan.

Azumin watan Ramadan, yana cikin shika-shikan Musuluci kuma al’ummar Musulmi sukan kauracewa ci da sha da saduwa da iyali tun daga fitowar al fijir har zuwa faduwar rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.