Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya zargi Obama da shirya zanga-zanga

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ya yi amanna cewa Barack Obama na da hannu wajen shirya zanga-zangar nuna adawa da ‘yan majalisun dokokin kasar karkashin Jam'iyyar Republican da kuma fallasa bayanan sirrin fadar White House.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka © REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta FOX, shugaba Trump ya ce, “ Ina tunanin shugaba Obama na da hannu cikin wannan lamari saboda mutanensa na da hannu.”

Trump ya kara da cewa, akwai kuma siyasa a cikin lamarin amma bai bada wata hujja ba dangane da ikirarin nasa.

‘Yan Majalisun na Republican na shan tambayoyi daga al’ummar da ta zabe su dangane da tsarin tafiyar da mulkin Trump.

Kawo yanzu dai tsohon shugaban na Amurka Barack Obama bai mayar wa Trump da martani ba.

Hirar da aka yi da Trump dai  zuwa ne ‘yan sa'oi gabanin jawabin da zai gabatar a gaban zaman hadin gwiwa na majalisun kasar biyu, in da ake saran zai bada cikakken bayanai game da shirinsa na takaita kashe kudi da kuma habbaka tattalin arzikin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.