Isa ga babban shafi
Syria

Majalisar dinkin duniya ta goyi bayan tsagaita wutar da Rasha ta samar a Syria

An shiga kwana na 2 ba a ji amon makamai ba a Kasar Syriya a karkashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin yan adawa da gwamnatin Bashar al Assad.

Ministocin harakokin wajen Iran, Rasha da Turkiya na taron manema labarai kan syria
Ministocin harakokin wajen Iran, Rasha da Turkiya na taron manema labarai kan syria Reuters
Talla

kasar Rasha ta samu amincewar komitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan yarjejeniyar tsagaita wutar da ta jagoranci samarwa, al’amarin da ya sake buda sabuwar turbar tattauna kawo karshen rikicin kasar.

Ayarjejeniyar da bata shafi yaki da ake yi da Kungiyar IS mai da’awar jihadi a kasar ba, zata bada damar a cikin watan janairun wannan shekara ta 2017 shiga tattauna neman zaman lafiya tsakanin gwamnati da yan tawaye a kasar kazastan, karkashin jagorancin kasashen Rasha da Iran dake goyon bayan gwamnatin Syriya, da kuma kasar Turkiya mai goyon bayan ‘yan tawaye a dai gefen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.