Isa ga babban shafi
MDD

Kasashe matalauta na ci gaba da tsiyacewa

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashe matalauta da ke duniya na ci gaba da tsiyacewa, kuma mawuyaci ne su farfado ba tera da samun karin tallafi da kuma inganta harkokin kasuwanci ba.

Har yanzu kasashen duniya matalauta na ci gaba da tsiyacewa
Har yanzu kasashen duniya matalauta na ci gaba da tsiyacewa AFP/ISSOUF SANOGO
Talla

Rahotan Majalisar ya ce, tun lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta shata sunayen kasashe fiye da 50 masu tasowa shekaru 45 da suka gabata, hudu ne kawai daga cikinsu suka tsallake shingen talauci da suka hada da Botswana da Cape Verde da Maldives da kuma Samoa.

Sauran kasashe 48 matalauta sun gaza samun ci gaba, yayin da kuma rabin talakawan duniya ke zaune a wadannan kasashen kamar yadda rahoton ya ce.

Majalisar ta ce, amma akwai fata mai kyau ga kasashe irin su Angola da Equatorial Guinea da Vanuatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.