Isa ga babban shafi
Haiti

Kwalera ta barke a Haiti bayan guguwar Matthew

Annobar cutar Kwalera ta barke a Haiti a yayin da kasar ke zaman makokin daruruwan mutanen da suka mutu sakamakon bala’in guguwar Matthew. Yanzu haka Kungiyoyin agaji ne ke ci gaba da aikin taimakawa wadanda bala'in guguwar ya shafa.

Guguwar Matthew ta yi barna da Cuba da Haiti da Jamhuriyyar Dominican
Guguwar Matthew ta yi barna da Cuba da Haiti da Jamhuriyyar Dominican RFI/Stefanie Schüler
Talla

Guguwar matthew ta kashe kusan mutane 1000 a Haiti, kuma yanzu akalla mutane 15 suka mutu sakamakon annobar cutar Kwallera da ta barke kasar.

Hukumomi a kasar sun yi gargadin cewa cutar za ta ci gaba da yaduwa saboda yadda guguwar Matthew ta haifar da gurbacewar muhalli a kasar.

Kwanaki hudu guguwar ta kwashe tana yin barna a yankin Caribbean, kuma yanzu ta tsallaka zuwa Amurka inda ta hallaka mutane biyar da kuma yin barna a jihohin Florida da Georgia da kudancin Carolina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.