Lagarde za ta kare kanta don kaucewa gurfanarwa
Yau shugabar hukumar bayar da Lamuni ta duniya Christine Lagarde za ta yi yunkurin karshe don ganin ta kaucewa gurfanarwa a gaban kotu saboda ta biya wani attajirin Faransa Bernard Tapie wasu kudaden gwamnati ta hanyar da bai kamata ba a lokacin da ta rike da ministar kudin Faransa
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wani alkalin kasar zai duba bukatar Lagarde ta soke hukuncin wata karamar kotu wadda ta bukaci gurfanar da tsohuwar ministar saboda yadda aka biya attajirin dala miliyan 433.
Idan an tabbatar da laifin da ake zargin ta da aikatawa, za ta biya tarar dalar Amurka dubu 16.
Duk da wannan shari’a, hukumar bada lamuni ta duniya ta bayyana Lagarde a matsayin wadda za ta ci gaba da rike shugabancin hukumar a wa’adi na biyu daga makon gobe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu