Isa ga babban shafi
Masar

An daure mutane 6 saboda kisan Bafaranshe a Masar

Kotun Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru bakwai ga wasu ‘yan kasar 6 bayan ta same su da laifin dukan wani Bafaranshe har ya rasa ransa a shekara ta 2013.

Marigayi Mr. Eric Lang
Marigayi Mr. Eric Lang LOIC VENANCE / AFP
Talla

Mutanen sun lakada wa Eric Lang mai shekaru 49 dukan ne a gidan yari bayan an kulle shi saboda samun sa da laifin yawo ba tare da katin shaida ba, sannan kuma yana amfani da bisa ta jebu.

Mr. Lang dai malami ne mai koyar da harshen Faransanci a birnin Alkahira yayin da iyalansa suka caccaki hukumomin Masar akan mutuwarsa.

Lauyoyin iyalan sun ce, bincike ya nuna cewa, an shafe tsawon sa'oi shida ana dukan marigayin da rodi kuma sun yi zargin jami’an 'yan sanda na da hannu a lamarin.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce, dama jami’an tsaron Masar na yawaita azabtar da fursunoni a gidan yari tare da kashe su, zargin da ma’aikatar cikin gidan kasar ta musanta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.