Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan ya yi kira ga musulmai akan ta'addanci

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bukaci takwarorinsa na kasashen musulunci da su kawo karshen rarrabuwan kawuna a tsakaninsu tare da tinkrar matsalar ta’addanci a duniya

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan. REUTERS/Murat Cetinmuhurdar/Presidential Palace Press Office
Talla

Erdogan ya yi wannan kiran ne a gaban shugabannin kasashen musulunci da ke gudanar da taron kwanaki biyu a birnin Santanbul, inda ya ce, babban kalubalen da ya kamata su tinkara shi ne, matsalar rarrabuwan kawuna.

Erdogan ya ce, musulamai ne ke shan wahala sakamakon rikicen rikicen da ake fama da su a wasu sassan duniya, yayin da ya caccaki kungiyoyin ISIS wadda ta kwace yankuna da dama a Syria da kuma Boko Haram da ta karbe ikon wasu wurare a Najeriya.

Taron wanda kungiyar musulmi ta duniya OIC ta shirya, ya samu halartar gwamnatocin kasashe 30 kuma batun rikicin Syria da Yemen ne ya fi daukan hankali.

Manyan baki a taron sun hada da sarki Salman na Saudiya da shugaban Iran, Hassan Rouhani da ake ganin ba sa ga maciji musamman a ‘yan kwanakin nan, inda rahotanni suka ce, shugabannin biyu sun yi musayar kalamai.

Turkiya dai na bukatar nuna matsayinta ne a tsakanin al’ummar musulmin duniya da aka kiyasta cewa yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 700, musamman a kasashen da suka taba kasance karkashin daular Usmaniyya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.