Isa ga babban shafi
Faransa

Valls ba zai soke ziyarsa a Algeria ba

Firaministan Faransa Manuel Valls, ya ce bai kamata sabanin da aka samu tsakanin hukumomin Algeria da kuma wasu kafafen yada labaran Faransa da aka hanawa wakilansu Visa shiga Algeria ya sa shi soke ziyarar aiki da ya shirya kai wa birnin Alger ba.

Manuel Valls da shugaba Abdelaziz Bouteflika na Algeria
Manuel Valls da shugaba Abdelaziz Bouteflika na Algeria Eric FEFERBERG / AFP
Talla

Hukumomi a Algeria sun hana wa wakilan kafafen yada labaran da ke shirin raka Valls a wannan ziyara wato Le Monde da kuma Canal+ takardar Visar shiga kasar, bayan da suka buga hoton shugaba Abdoul Aziz Boutefilka a shafukansu na farko, domin kawata labarin bayyanan sirri na Panama, duk da cewa ba sunan shugaban a cikin wadanda ake zargi.

Manuel Valls wanda ya isa Algeria tun ranar Asabar da ta gabata, ya gana da takwaran aikinsa na kasar Abdel Malek Sellal da kuma shugaba Abdoul Aziz Bouteflika, kafin daga bisani ya halarci wani taron hadin-guiwa na tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu a birnin Algers.

To sai dai kafafen yada labarai da dama na Faransa sun ki nunawa ko kuma yada wannan ziyara ta Valls, domin bayyana bacin ransu dangane da hana wakilan jaridar Le Monde da wata karamar jarida da ake kira Canal+ Visa da hukumomin Algeria suka yi, bayan da wadannan jaridu suka buga hoton shugaba Bouthfilka a shafukansu na farko, domin kawata labarin bayanan sirri na Panama, duk da cewa ba sunan shugaban na Algeria a cikin wadanda ake zargi a tonon sililin.

A lokacin da yake zantawa da menama labarai a birnin Algers, Manuel Valls ya ce, ba shi da niyyar soke kai wannan ziyara sakamakon sabanin da aka sama tsakanin ‘yan jaridun da hukumomin Algeria, domin kuwa Algeria kasa ce mai muhimmanci ta fannoni daban daban ga Faransa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.