Isa ga babban shafi
Amurka

John Kerry na ziyarar a Hiroshima na Japan

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya fara ziyarar aiki ta yini biyu a birnin Hiroshima na kasar Japan tare da sauran ministocin waje na kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya.

Sakataren harkokin wajen Amurka a ziyarsa ta yini biyu a Hiroshima na Japan
Sakataren harkokin wajen Amurka a ziyarsa ta yini biyu a Hiroshima na Japan
Talla

Wannan ne dai karo na farko tun bayan yakin duniya na biyu, da sakataren harkokin wajen Amurka ya kai ziyara a wannan gari, inda Amurka ta taba yin amfani da makamin nukilya a ranar 6 ga watan Agustan shekarar 1945 inda aka samu asarar rayukan mutane dubu 140 a garin na Hiroshima kawai.

Masharhanta na ganin cewa wannan ziyara ta Kerry alama ce da ke nuna cewa, da yiwuwar Amurka ta bayar da hakuri a hukumance sakamakon asarar rayukan da ta haddasa bayan jefa makamin nukiliya, amma Mr. Kerry ya yi watsi da hasashen.

Mr. Kerry ya bayyana jin dadinsa kasancewarsa sakataren wajen Amurka na farko da ya ziyarci garin tun bayan aukuwar lamarin.

Ana sa ran shi ma shugaban Amurka Barack Obama zai kai irin wannan ziyarar nan gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.