Isa ga babban shafi
Armenia-Azerbaijan

Turkiya na rura wuta rikici tsakanin Armenia da Azerbaijan

Tun a ranar Juma’a ne dai dakarun Armenia da Azerbaijan ke gwabza fada kan ikon yankin Nagorno-Karabakh.A jiya kimanin mutane 13 suka mutu a kwana na uku da dakarun kasashen biyu ke rikici. 

Yankin da ake gwabza fada tsakanin Armenia da Azerbaijan
Yankin da ake gwabza fada tsakanin Armenia da Azerbaijan REUTERS/Vahram Baghdasaryan
Talla

Rasha da kasashen yammaci sun yi kiran kawo karshen rikicin tare da zargin Turkiya da rura wuta.
Wannan na zuwa ne bayan kalamin Shugaban Turkiya Recerp Tayyip Erdogan da ya ce a kwana a tashi wata rana sai yankin Nagorno ya dawo ikon Azerbaijan.
Zuwa yanzu kimanin mutane 46 suka mutu, kuma tun a 1994 Armenia ke rikici da Azerbaijan kan Nagorno bayan sun yi watsi da yarjejeniyar da suka amince ta sulhu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.