Isa ga babban shafi
panama

An tona asiran shugabannin duniya

Wasu takardun sirri da aka fitar a kasar Panama sun bayyana cewa, shugabannin kasashen duniya da ‘yan wasa da jaruman fina-finai da kuma amshakan masu kudi na cikin wadanda ke boye kudadensu a kasashen ketare don kauce wa biyan haraji da kuma halarta kudaden haram.

Ofishin alkalai a Panama mai suna Mossack Fonseca  ya fitar da takardun sirrin a ranar Lahadi.
Ofishin alkalai a Panama mai suna Mossack Fonseca ya fitar da takardun sirrin a ranar Lahadi. t13.cl
Talla

Sama da kafafan yada labarai guda 100 ne suka gudanar da bincike akan wannan al’amari da aka bayyana a matsayin abin kunya da kuma ake ganin shi ne babban tonon silili da aka taba samu a tarihi.

Kafafan yada labaran sun binciki sakwannin na e-mail na sama da shekaru 40 da suka gabata da kuma takardun bayanan kudade har ma da bayanan fasfo-fasfo daban daban, abinda ya nuna yadda wadannan mutane suka adana kudadensu a wasu kasashen ketere.

Takardun sirrin wadanda wani ofishin alkalai a Panama mai suna Mossack Fonseca ya fitar, sun nuna cewa wasu bankuna da kamfanoni da ke da alaka da shugaban Rasha Vladmir Putin sun karkata alakar kudaden da yawansu ya kai Dalar Amurka biliyan 2, inda suka adana su a wasu kamfanonin kasashen waje.

Shi ma firaministan Iceland, Sigmundur David da matarsa na cikin wadanda ake zargi, inda suka yi amfani da wani kamfanin ketare wajen adana miliyoyin Dala a dai dai lokacin da Iceland ke fama da matsalar rashin kudi.

Sauran da ake zargi sun hada da firaministan Pakistan da shugaban kasar Ukraine da sarki Abdallah na Saudiya da iyalan shugaban kasar China Xi Jinping da kuma mahaifin firaministan Birtaniya David Cameron da Lionel Messi, shahararren dan wasan kwallon kafa a duniya da kuma fitaccen jarumin fina-finai Jakie Chan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.