Isa ga babban shafi
MDD-Masar

'Yan rajin kare hakki na cikin wani hali a Masar

Majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama da suka hada da Human Rights Watch da Amnesty International, sun bukaci kasar Masar da ta dakatar da sabuwar tuhumar da ta fara yi wa masu rajin kare hakkin dan Adam, abinda ya haifar da tsamin dangantata tsakanin Masar da Amurka.

Kwamishinan hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad Zeid al-Hussein.
Kwamishinan hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad Zeid al-Hussein. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Tun lokacin da aka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi a shekara ta 2013, hukumomin Masar suka jagoranci murkushe dukkanin masu adawa da gwamnati da suka hada da magoya bayan Morsi da kuma masu rajin kare hakkin dan Adam a kasar.

Kungiyoyin dai sun sha caccakar hukumomin Masar bisa tsare jama’a a gidajen yari ba bisa ka’ida ba da kuma batar da ‘yan rajin kare hakkin fararan hula tare da azzaba su.

Kwamishinan hukumar kare hakkin bil Adama ta majalisar dinkin duniya, Zeid Ra’ad ya bayyana cewa, ci gaba da keta hakkin fararen hula zai ragewa kungiyoyi masu zaman kansu armashi duk da cewa suna taka rawa wajen tattara bayanai kan cin zarafin al’umma tare da nuna goyon baya ga duk wanda aka zalunta.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin suka fitar, Amnesty International ta ce, ana daukan kungiyoyin fafaren hula na Masar a matsayin makiyan gwamnati, mai makon a dauke su a matsayin abokan samar da sauye sauye da ci gaba a kasar.

Rahotanni sun ce, a kwanan nan ne hukumomin Masar suka tuhumi ma’aikatan kare hakkin dan Adam, sannan kuma suka hana su tafiye tafiye baya ga yunkurin kwace kadarorinsu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.