Isa ga babban shafi
faransa-Iran

Faransa ta bukaci a sanyawa Iran Takukumai

Faransa ta ce akwai yiyuwar sanyawa Iran wasu takunkumai bisa gwajin makamai masu linzami da kasarta yi a makon da ya gabata.

Ministan harkokin wajen Faransa  Jean-Marc Ayrault da Takwaransa na Amurka John Kerry
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da Takwaransa na Amurka John Kerry REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ne ya sanar da bukatar sanyawa Iran takunkumi bisa sabon gwajin makamai masu linzami da kasar ta yi a makon da ya gabata.

Ayrault ya sanar da hakan ne bayan ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da sauran takwarorinsa na kasashen Turai.

Ministan ya kara da cewa gwajin makaman da Iran ta yi ya zarta ka’aida, abinda ke iya zama babban barazana ga kasashen yankin da sauransu.

Sai dai kuma hukumar da ke kula da makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Iran ba ta sabawa yarjejeniyar da ta kula da sauran kasashen duniya a watan Yulin bara ba.

A yayin da a na ta bangaren kasar ta Iran ta kare tsarin nukiliyarta da kuma gwajin da cewa ba barazana ba ce ga kasashen Duniya kamar yadda ake tunani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.