Isa ga babban shafi
Spain

An kama kwantenonin masu jihadi a Spain

‘Yan sanda a kasar Spain sun sanar da kama wasu kwantenoni guda uku makare da kakin soja, wanda a cewar hukumomin kasar ana shirin wucewa da su ne domin rabawa masu da’awar jihadi a kasashen Syria da Iraqi.

An kama kwantenonin ne a tashar jirgin ruwan Spain makare da kakin soja domin turawa mayakan jihadi a Syria da Iraqi.
An kama kwantenonin ne a tashar jirgin ruwan Spain makare da kakin soja domin turawa mayakan jihadi a Syria da Iraqi. D.R.
Talla

An dai gano wadannan kwantenoni ne a tashoshin jiragen ruwa biyu da ke gabashin kasar, lokacin wani samame da ‘yan sanda suka kai domin kama shugabannin wata kungiya da ta shahara wajen aikewa da makamai da sauran kayan fada ga kungiyiyoyin da ke ikirarin yin jihadi.

A da can, Kungiyoyin na bayyana kansu ne a matsayin wadanda ke tattara kayayyakin jinkai domin turawa zuwa kasashen da ke fama da rikici, kuma ta haka ne suke fakewa domin boye makamai ga irin kungiyoyin na ta’addanci.

Da farko dai an gabatar da wadannan kwantenoni ne a matsayin wadanda ke kunshe da tsoffin tufafi da za a tura zuwa Syria da Iraqi domin rabawa jama’ar da ke cikin mawuyacin hali, to sai dai bincike ya gano cewa tufafin soji ne har guda dubu 20.

To sai dai wani abin lura a game da wannan lamari, daya daga cikin mutane 7 da ‘yan sanda suka kama, shugaban wani kamfani ne da ya shahara ta fannin fitar da tsofaffin tufafi zuwa kasashen ketare daga Spain.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.