Isa ga babban shafi
Syria

Majalisar Dinkin Duniya Ta Fara Jefawa Mabukata Abinci a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa ta sami jefa kayayyakin jinkai da jiragen sama ga dubban ‘yan kasar Syria dake fama da matsanancin karancin abinci, a wani gari dake hannun kungiyar IS masu ikirarin jihadi.

Sakatare Janar na MDD Ban Kimoon
Sakatare Janar na MDD Ban Kimoon © REUTERS/Lucas Jackson
Talla

A cewar Stephen O’Brien, Jami’in bada kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya wani jirgin sama na dakon kaya ya jejjefa ton 21 na kayan abinci a garin Deir Ezzor dake gabashin Syria.

Wasu jami'an dake yankunan sun gaskata cewa anyi nasarar jefa wa jama’a kayan agaji.

Wasu majiyoyin na cewa ana ta kokarin ganin zuwa Juma'a kayayyakin jinkai sun kai ga karin mutane dake cikin wani hali a kasar.

A watan jiya Rasha ta sanar da cewa ta jefa irin wadannan kayayyakin jinkai a garin Deir Ezzor, inda ake da mutane akalla dubu 200 dake cikin mawuyacin halin rashin abinci da magunguna, tun lokacin da mayakan kungiyar dake ikirarin jihadi ta IS suka yiwa yankin kofar rago.

A cewar jami'in Jinkai na MDD akwai wasu mutane dubu 110 dake garuruwan dake kusa da yankin da suka sami dan abin da zasu sa a bakin salati, amma har ila yau akwai wasu mutanen dubu 230 dake bukatar taimako.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.