Isa ga babban shafi
Real Madrid

Zidane ne sabon Kocin Real Madrid

Zinedine Zidane ya yi alkawalin yin aiki tukuru domin ciyar da Real Madrid gaba bayan kungiyar ta nada shi sabon koci sakamakon sallamar Rafa Benitez.

Sabon Kocin Real Madrid Zinédine Zidane
Sabon Kocin Real Madrid Zinédine Zidane AFP PHOTO/ GERARD JULIEN
Talla

Zidane ya sha alwashin lashewa Real Madrird kofi a bana duk da kungiyar a yanzu tana matsayi na uku ne a teburin La liga.

A jiya Litinin ne Real Madrid ta sallami Rafael Benitez, duka watanni bakwai da ba shi aikin horar da kungiyar bayan korar Carlo Ancelotti.

Benitez ya fuskanci kalubale tun dukan da Barcelona ta yi wa Madrid a kakar bana ci 4 da 0.

Sannan daga baya aka yi waje da Madrid a gasar Copa del Ray karkashin jagorancinsa.

An kori Madrid a Copa del Ray ne saboda Benitez ya yi amfani da Dan wasan da bai dace ba.

Korar Benitez kuma na zuwa ne bayan Valencia ta rike Madrid ci 2 da 2 a ranar Lahadi, matakin da ya kara tazara tsakaninta da Atletico Madrid da ke saman teburin la Liga.

Tun bayan kamala wasan Clasico magoya bayan Real Madrid suka yanke kauna da Benitez.

Babu dai bayani akan yarjejeniyar da Zidane ya kulla da Madrid, amma shi ne koci na 11 da shugaban kungiyar Florentino Perez ke dauka a shekaru 12.

Yanzu ido ya koma ga Zidane, ko yana da kwarewar da zai iya biya wa Real Madrid bukatunta na lashe kofi?

Zidane dai tsohon dan wasan Real Madrid ne wanda ya rubuta sunansa a tarihin kungiyar musamman kwallon da ya jefa a ragar Bayer Leverkusen wanda da ya ba kungiyar nasara a wasan karshe a gasar zakarun Turai a shekarar 2002.

Kuma tun a 2009 ne shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ba shi aikin mai bayar da shawara, sannan a 2011 aka nada shi Darakta.

Zidane kuma ya yi mataimakin koci ga Carlo Ancelotti a 2013 zuwa 2014. Daga baya kuma aka nada shi kocin karamar kungiyar Real Madrid da ake kira Castilla duk da ba ya da wata kwarewa ga aikin horar da ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.